IQNA

Ministan Faransa: Babu Alaka Tsakanin Ta'addanci Da Muslunci

22:50 - March 01, 2017
Lambar Labari: 3481273
Bangaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana cewa, babu wata alaka a tsakanin addinin musulunci da ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Jaridar Jakarta Club ta bayar da rahoton cewa, a ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ta Faransa yake gudanarwa a kasar Indonesia, kasar musulmi wadda tafi sauran kasashen msuulmi yawan jama'a, ya bayyana cewa ayyukan ta'addanci daban addinin muslunci daban.

Dangane da irin yadda ake takura musulmi a kasashen turai da nuna musu kyaa kuwa, ministan na Faransa ya bayayna cewa kasar Faransa tana kallon 'yan kasarta a matsayin al'umma guda, ba tare da nuna wani banbanci a tsakanin addinai, domin a cewarsa kowane mutum yana da hakkin ya bi addinin da yake so ko akidar da ya ga dama.

Ya bayyana ayyukan ta'addanci a matsayin abin da ke barazana ga daukacin kasashen turai, da na asia da kuma yankin gabas ta tsakiya.

captcha