Tarukan tunawa da ranar shahadar Imam Ridha (AS) a Mashhad, Qum, da Shiraz
Tehran (IQNA) An gudanar da zaman makoki na zagayowar ranar shahadar Imam Ridha (AS) a wurare masu tsarki na Mashhad, Shiraz, da Qum.
Al'ummar Iran sun gudanar da zaman makoki na zagayowar ranar shahadar Imam Riza (AS), Imamin Ahlul bait na takwas, a ranar 27 ga Satumba, 2022, a fadin kasar.