IQNA

Yahudawan Moroko sun yi tir da wulakanta wani masallaci a Jenin

16:19 - December 19, 2023
Lambar Labari: 3490335
Yahudawan Moroko sun yi Allah wadai da matakin da sojojin yahudawan sahyoniya suka dauka na wulakanta wani masallaci a Jenin.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press B cewa, yahudawan Moroko sun yi Allah wadai da matakin da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suka dauka na wulakanta wani masallaci a garin Jenin.

Bayan harin da aka kai wa Jenin, wasu gungun sojojin Isra'ila sun shiga wani masallaci inda suka karanta addu'a ta musamman ga Yahudawa.

Bidiyon wannan mataki na sojojin yahudawan sahyoniya ya yadu a shafukan sada zumunta inda ya biyo bayan martani da tofin Allah tsine.

Bayan wannan lamarin, ministan tsaron kasar Itamar Ben Goyer ya kai wa ministan tsaro Yoav Galant hari kan shawarar da ya ce: "An yi Allah wadai da shigar da siyasa cikin soja." Dole ne mu gode da kuma yaba wa sojojinmu; Domin sun yi kasada da rayukansu a Jenin kuma hukuncin da aka yanke yana cutar da kwarin gwiwar sojojinmu.

Dangane da haka, Ishak Youssef, babban malamin Isra'ila, ya aike da wasika zuwa ga Eyal Karim, babban limamin sojojin Isra'ila, game da halayen sojojin Isra'ila a lokacin shiga masallatai da gidajen Falasdinawa.

A cikin wannan sakon, ya rubuta cewa: Matukar dai ba a bukatar yaki, babu wanda ya isa ya yi tada hankali. Musamman idan batun ya shafi lamurran addini.

Ya kara da cewa: Dole ne mu fahimtar da wadannan sojoji cewa bai halatta a rinjayi tunanin addini na mabiya sauran addinai ba.

Shi ma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya yi tsokaci game da wannan lamarin inda ya ce a wani taron manema labarai da ya kira: "Mun damu da wadannan hotuna." Wannan mataki ne da bai dace ba. Ko da yake rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta dauki matakai kan wadannan sojoji.

 

4188684

 

captcha