IQNA

Majalisa ta Amince da yin Allah wadai da ‘yar majalisa saboda goyon bayan Falastinu

14:26 - November 08, 2023
Lambar Labari: 3490115
Washingto (IQNA) Majalisar Wakilan Amurka ta amince da daftarin kudirin yin Allawadai da ‘yar majalisar wakilai ‘yar asalin Falastinu     Rashidah Tlaib, daga Michigan, bisa goyon bayan al’ummar Palasdinu.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a jiya ne majalisar wakilan Amurka da ke karkashin jagorancin ‘yan jam’iyyar Republican ta kada kuri’ar yin Allah wadai da Rashida Tlaib, ‘yar jam’iyyar Democrat daga Michigan, wadda ‘yar asalin Falasdinu ce. Tlaib ta soki Isra'ila da kakkausar murya a cikin 'yan kwanakin da suka gabata kuma a daidai lokacin da take ci gaba da kai harin bam a Gaza.

Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri'a 234 zuwa amma an amince da 188 don yin Allah wadai da Rashida Tlaib, wakiliyar Democrat, saboda yada labaran karya game da harin kungiyar Hamas kan Isra'ila da kuma amfani da kalmar "Falastinu daga kogi zuwa teku". Wasu sun fassara shi a matsayin kira na kawo karshen wanzuwar Isra'ila. Ya zuwa yanzu, mambobin Majalisar Wakilan Amurka uku ne aka yanke musu irin wannan hukunci daga 2021.

Fiye da Falasdinawa 10,000 ne aka kashe tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza wata guda da ya wuce. Amurka, mai goyon bayan Isra'ila ido rufe, ta bijirewa kiran da aka yi na tsagaita bude wuta a daidai lokacin da duniya ke ci gaba da nuna bacin rai game da batun matsalolin jin kai da ake fama da su a yankin zirin Gaza mai mutane miliyan 2.3.

 

4180616

 

captcha