Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a rana ta 18 ta hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a zirin Gaza, ana ci gaba da kokarin masu ruwa da tsaki na siyasa da cibiyoyi na kasa da kasa na yin tasiri a kan al’amuran da ke faruwa a yankin.
A daya hannun kuma, sojojin Isra'ila sun yi ikirarin kai hari kan wuraren soji sama da 400 da damammakin ababen more rayuwa da wuraren taruwa na dakarun Hamas cikin sa'o'i 24 da suka wuce.
A gefe guda kuma, ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta sanar da cewa, tun bayan fara harin Hamas da guguwar Al-Aqsa a yankunan da ta mamaye, 'yan Isra'ila 5,400 ne suka jikkata, wadanda 40 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Sukar da Obama ya yi a fakaice kan laifukan Isra'ila
Tsohon shugaban na Amurka ya yi gargadin cewa wasu ayyukan Isra'ila a yakin da suke yi da kungiyar Hamas, kamar katse abinci da ruwan sha ga fararen hula na Gaza, na iya yin mummunar illa ga dabi'un Falasdinu na yara masu tasowa.
A cikin wata sanarwa da aka buga a kan Medium, Obama ya rubuta cewa: Wadannan ayyuka za su iya rage goyon bayan duniya ga Isra'ila, haifar da cin zarafi daga abokan gaba na Isra'ila, da kuma lalata kokarin da aka dade na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.