A rahoton Falasdinu Ilyum, a yau tsakar rana ne gwamnatin yahudawan sahyoniya ta fara kai sabbin hare-hare kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.
A cewar majiyoyin kiwon lafiya akalla mutum guda ne ya mutu sakamakon harin da mayakan gwamnatin sahyoniyawan suka kai a gabashin Khan Yunis, inda suka auna wasu gungun manoma a gonakinsu.
A halin da ake ciki dai gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hari a yankunan Al-Qararah da Absan al-Kabirah da ke gabashin Rafah da kuma arewacin zirin Gaza, inda aka yi shahada daya da jikkata wasu da dama, kuma akalla yara biyu na daga cikin wadanda suka jikkata.