IQNA

Neman shiga tsakani na duniya don kare Masallacin Al-Aqsa

23:13 - March 08, 2023
Lambar Labari: 3488775
Tehran (IQNA) Ma'aikatar harkokin wajen kasar Falasdinu ta yi kira da a gaggauta shiga tsakani na kasa da kasa domin dakile harin da aka kai wa Masallacin Al-Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Rai Alyoum ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinu ta yi kira da a gaggauta shiga tsakani na kasa da kasa domin dakile harin da ake kai wa masallacin Al-Aqsa tare da gargadi kan kiraye-kirayen kai hari kan masallacin a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da Yahudawa na Purim.

Ma'aikatar ta jaddada a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin yau cewa, wadannan kiraye-kirayen na tunzura jama'a da hare-hare na tunzura jama'a sun samo asali ne sakamakon kafa gwamnati mai ra'ayin mazan jiya wacce aikinta shi ne tada zaune tsaye a kasar Falasdinu da kuma haifar da rikici a jere.

Ma'aikatar harkokin wajen gwamnatin Falasdinu ta dauki gwamnatin yahudawan sahyoniya a matsayin cikakken alhakin kai hare-haren da aka kai a Masallacin Al-Aqsa.

 

4126847

 

 

captcha