Galibin kasashen msuulmi dai sun sanar da yau a matsyin ranar idin karamar sallah, daga cikin kasashen da suka yi sallah a yau dai har da Saudiyya Masar Aljeriya Najeriya da sauransu.
Wannan yana zuwa nea daidai lokacin da wasu daga cikin kasashen musulmi suka sanar da yau Litinin a matsayin ranar 30 ga watan Ramadan, wato rana ta karshe a wanann wata mai alfarma, bayan da suka sanar da cewa ba su samu damar ganin jinjirin watan shawwala a yammacin jiya Lahadi ba.
Daga cikin kasashen da suka sanar da Ranar gobe Talata a matsayin ranar idin karamar Sallah, har da kasar Iran, da kuam kasashen Pakistan, Bangaladesh, India da kuma Iraki.
Sai dai kuma tun a ranar jiya Lahadi wasu daga cikin kasashen musulmi sun yin sallar idi, bayan da suka ga watan a yammacin Asabar da ta gabata, daga cikin kasashen kuwa har da Jamhuriyar Nijar, Jordan, Morocco da kuma Afghanistan.