IQNA

Sheikh Khalid Mulla: Yakin Yaman ba ya da fa'ida ga maharan

20:59 - February 05, 2022
Lambar Labari: 3486910
Tehran (IQNA) Sheikh Khalid Mullah shugaban majalisar malaman ahlu sunna na Iraki ya bayyana cewa, yakin kasar Yemen ba shi da wani amfani ga kowa.

Shugaban majalisar malaman ahlu sunna na Iraki Sheikh Khalid Mullah ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Saudiyya ke jagoranta kan al'ummar kasar Yemen.

Ya ce babu wanda ya ke amfana da kuma yin murna da wanann yaki illa makiya muslunci, domin kuwa musulmi ne suke yakar kasar 'yan uwansu musulmi, suke kashe 'yan uwansasu , suke ruguza kasar musulmi.

Shehin malamin ya ci gaba da cewa, daga lokacin da Saudiyya ta fara kaddamar da yaki kan al'ummar Yemen shekaru bakawai da suka gabata ya zuwa babu abin da ta cimmawa, in banda kashe dubban fararen hula mata da kananan yara a Yemen, tare da rusa daruruwan masallatai, da makarantu da asibitoci da kasuwanni.

Daga karshe ya yi kira ga Saudiyya da ta sake tunani kan kisan musulmin kasar Yemen da take, domin kuwa goyon bayan da take samu daga Amurka da Burtaniya da yahudawan Isra'ila ba zai kare ta daga wannan abin kunya ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4034015

captcha