IQNA

Gwamnatin Yahudawan Isra'ila Ta Bude Ofishin Jakadanci A Bahrain

21:38 - October 01, 2021
Lambar Labari: 3486370
Tehran (IQNA) gwamnatin yahudawan Isra'ila ta bude ofishin jakadanci a birnin Manama na Bahrain.

Tashar Alarabiya ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin yahudawan Isra'ila ta bude ofishin jakadanci a birnin Manama na Bahrain.

Lapid ya kaddamar da ofishin jakadancin Isra'ila a Manama, sannan kuma ya tattauna da takwaransa na Bahrain a kan batutuwa da suka shafi kara karfafa alaka tsakanin gwamnatin Bahrain da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Bahrain da Isra’ila sun sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar kulla alaka a ranar 11 ga watan Satumban shekarar da ta gabata, wanda hakan ya sanya Masarautar ta zama kasa ta hudu ta Larabawa da ta rattaba hannu kan irin wannan yarjejeniyar tare da Isra’ila, bayan Masar da hadaddiyar daular larabawa.

Haka ann kuma baya ga Bahrain, wasu daga cikin kasashen larabawa sun bi sahun sauran kasashen da suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila daga baya-bayan nan, da suka hada da gwamnatin Morocco, da kuma gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan.

Al'ummar Bahrain sun gudanar da zanga-zanga a dukkanin fadin kasar domin nuna rashin amincewa da wannan ziyara ta ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra'ila, da kuma kin amincewa da bude ofishin gwamnatin yahudawa a kasarsu.

 

 

4001478

captcha