IQNA

Ministan Harkokin Wajen Gwamnatin Yahudawan Isra'ila Na Gudanar Da Ziyara A Bahrain

18:14 - September 30, 2021
Lambar Labari: 3486368
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra'ila ya isa kasar Bahrain.

A yau ne ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra'ila Yair Lapid ya isa birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain.

 

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, bayan isarsa birnin Manama ministan harkokin wajen Isra’ila Yair Lapid ya samu tarba daga sarkin kasar Bahrain a fadarsa.

Lapid ya kaddamar da ofishin jakadancin Isra'ila a Manama, sannan kuma ya tattauna da takwaransa na Bahrain a kan batutuwa da suka shafi kara karfafa alaka tsakanin gwamnatin Bahrain da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Bahrain da Isra’ila sun sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar kulla alaka a ranar 11 ga watan Satumban shekarar da ta gabata, wanda hakan ya sanya Masarautar ta zama kasa ta hudu ta Larabawa da ta rattaba hannu kan irin wannan yarjejeniyar tare da Isra’ila, bayan Masar a 1979, Jordan a 1994, da UAE a 2020.

Baya ga Bahrain, wasu daga cikin kasashen larabawa sun bi sahun sauran kasashen da suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila daga baya-bayan nan, da suka hada da gwamnatin Morocco, da kuma gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan.

 

 

captcha