IQNA

Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Ya Isa Morocco

21:55 - August 11, 2021
Lambar Labari: 3486191
Tehran (IQNA) ministan gwamnatin yahudawan sahyuniya ya isa kasar Morocoo.

Tashar akhabr Quds ta bayar da rahoton cewa, Yair lapid ministan gwamnatin yahudawan sahyuniya ya isa kasar Morocoo a yau Laraba.

Ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan ya isa kasar Morocco ne tare da rakiyar ministan jin dadin jama'a na yahudawan Isra'ila, inda suka samu gagarumin tarbe daga gwamnatin Morocco.

Lapid ya bayyana wannan rana da cewa ta tarihi ce ga Isra'ila, domin kuwa wannan yana nuni da irin karbuwar da Isra'ila take samu daga gwamnatocin larabawa.

Ministan yahudawan ya gana da takwaransa na Morocco, tare da sanya hannu a kan wasu yarjeniyoyi na yin aiki tare tsakanin gwamnatin Morocco da kuma gwamnatin yahudawan Isra'ila..

Morocco dai ta sanar da amincewa da Isra'ila a hukumance sakamakon matsin lambar da ta fuskanta daga gwamnatin Trump, tare da yi mata alkawalin cewa idan ta yi hakan, Amurka za ta amice da yankin yammacin Sahara a hukuamnce da cewa mallakin kasar Morocco ne.

 

 

3990157

 

captcha