IQNA

An Nuna Wani Dadden Kur’ani Da Aka Kayata Da Ruwan Zinari A Taron Baje Kolin Abu Dhabi

22:57 - May 29, 2021
Lambar Labari: 3485960
Tehran (IQNA) an nuna wani kwafin kur’ani da aka kayata da ruwan zinari a taron baje koli a birnin Abu Dhabi.

Shafin yada labarai na al-ain ya bayar da rahoton cewa, a taron baje koli a birnin Abu Dhabi, an nuna wani kwafin kur’ani da aka kayata da ruwan zinari, wanda yake da dadadden tarihi.

An dai rubuta wannan kwafin kur’ani ne tun a karni na 11, wato  fiye da shekaru dari 9 da suka gabata, wanda kasafai ake samun irinsa ba.

A wannan baje kolin ana nuna tsoffin littafai da aka rubuta tun daga karni na 11 har zuwa karni na 19.

Babban daraktan cibiyar adana kayan tarihi ta Adina Gratis da ke kasar Austria, yana daga cikin wadanda suke jagorantar wannan baje koli.

An dai gina wannan cibiya ne tun a cikin shekara ta 1949, inda wannan cibiya take nemo muhimman kayan tarihi musamman littafai da aka rubuta tsawon shekaru da suka gabata.

Wasu daga cikin wadannan littafai an rubuta su ne a cikin kasashen turai da suke magana kan tarihi, amma da dama daga cikinsu an rubuta su ne a kasashen larabawa da na musulmi tsawon shekaru da suka gabata.

3974129

 

 

 

captcha