IQNA

An Fara Jarabawar Sharar Fage Ta Gasar Kur’ani Ta Duniya A Masar

21:22 - January 30, 2021
Lambar Labari: 3485603
Tehran (IQNA) an fara jarabawar share fage ta gasar kur’ani ta duniya a yankin port Saeed a kasar Masar.

Shafin yada labarai na Albawwaba News ya bayar da rahoton cewa, ofishin gwamnan lardin Port Saeed a kasar Masar ya bayar da bayanin cewa, an bude zaman yin jarabawa da bayar da horo ga wadanda za su shiga gasar kur’ani ta duniya.

Wannan dai shi ne na karo na uku da lardin Pors saeed a kasar Masar ke daukar nauyin wannan gasa, wadda take samun halartar makaranta da mahardata daga sassa na duniya.

A wannan karon dai sakamakon bullar cutar corona, wannan gasa ta kasa da kasa za a gudanar da ita ne ta hanyar alluna da suke dauke da hotunan bidiyo kai tsaye ta hanyar yanar gizo.

Daga cikin wadanda suke jagorantar shirin jarabawar da kuma tantancewa akwai Abdulkarim Saleh, shugaban bangaren tsare-tsare na jami’an Azhar, sai kuma Sheikh Abdulfattah Tarouti, fitaccen makaranci na duniya, kuma malami a cibiyar Azahar.

Wakilan kasashe 41 ne za su halarci gasar, daga yankunan Asia, da turai gami da Amurka da latin da kuma Afirka gami da yankin gabas ta tsakiya, a wanann karon daga cikin kasashen da za su halarta akwai Rasha, Burtaniya, sai kuma Malaysia da Indonesia da sauransu.

3950533

 

 

captcha