Kamfanin dilalncin labaran iqna, Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a yau Babban malamin addinin musl;ucni an kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Qasem ya isa birnin Najaf na kasar Iraki domin gudanar da ziyarar a wurare masu tsarki na birnin na ma wasu biranen na daban.
Ayatollah Isa Qasem ya isa birnin na Najaf daga birnin London na kasar Birtaniya inda yake karbar magani a asibiti, sakamakon rashin lafiya da yake faa da ita.
Tawagar da ke tare da shehin malamain ta sanar da cewa, wannan ziyara ba ta da wata alaka da gwamnatin Iraki, manyan malaman addini na kasar Iraki ne suka gayyace shi domin ya kawo ziyara, shi ne ya karba goron gayyatarsu.
Bayanin ya kara da cewa, byan ammala ziyara abirnin Najaf da kuma ganawac da manyan malaman addini da ke birnin, Ayatollah Isa Qasem zai nufi birnin Karbala, domin yin ziyara a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke birnin na Karbala.