IQNA

An Kakkabo Jirgin Yakin Haramtacciyar Kasar Isra'ila A Golan

18:46 - February 10, 2018
Lambar Labari: 3482383
Bangaren kasa da kasa, Dakarun tsaron sararin samaniyar kasar Siriya sun kakkabo jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra'ila samfarin F-16 a wannan Asabar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto kafafen yada labaran kasar siriya a safiyar yau Asabar na cewa sojan dake tuka jirgin yakin isra'ila ya hallaka bayan da sojojin tsaron sararin samaniyar kasar suka kakkabo jirgin a jijjifin safiyar yau Asabar.

Kafafen yada labaran yahudawan Isra'ila sun watsa labarin cewa jirgin yakin da Siriya ta harbo ya mayar da martani ne bayan da Sojojin siriya suka harba rokoki biyar a tudun Golan a daren jiya juma'a.

Kamfanin dillancin labaran Rusuya Alyaum ya habarta cewa Sojojin tsaron sararin samaniyar Siriya sun harbo jirgin yakin Isra'ilan ne bayan da ya kai wasu hare-hare a cikin kasar ta Siriya.

A nata bangare, gwamnatin yahudawa ta tabbatar da faduwar jirgin yakinta na sannan ta ce ya fadi ne a cikin kasar ta.

3690143

 

 

 

 

 

 

 

captcha