IQNA

An Kai Hari Kan Cibiyar Muslunci A Canada Tare Da Kone Kur'ani

22:27 - October 13, 2016
Lambar Labari: 3480853
Bangaren kasa da kasa, masu iyayya da muslunci sun kaddamar da hari kan cibiyar musulmi da ke lardin Queensland a kasar Canada.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Sabah cewa, harin da aka kai kan cibiyar muslunci a lardin queensland ya zo ne a daidai lokacin kyamar muslunci ke ci gaba da karuwa akasar.

Kafin wannan lokacin dai an lika wasu fastoci ne da suke dauke da hotuna da kuma zanen batunci ga addinin muslunci a kan bangaye a sassa na lardin, kafin daga bisania kaddamar da hari.

Karuwar hare-haren kan musulmi dai sakamako na ayyukan ta'addanci da kungiyoyi masu akidar kafirta musulmi irin su Daesh suke aikatawa, wanda hakan ya sanya da dama daga cikin mutane suke kallon muslunci a haka.

A cikin yan watannin da suka gabata ne dai shugaban cibiyar musulmin yankin queensland ya bayyana cew, kai hari kan musulmi ba abu ne da za a amince da shi ba, domin kuwa ya sabawa dokokin kasar kamar yadda kuma ya sabawa yan adamka.

3537492


captcha