IQNA

Kasashen Turai Da Suke Da Kyakkyawar Fahimta Dangane Da Musulmi

23:26 - May 30, 2017
Lambar Labari: 3481566
Bangaren kasa da kasa, wani sakamakin bincik ya nuni da cewa akwai wasu kasashe daga cikin kasashen turai wadanda fahimtar ta dara ta sauran a kan musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin pewresearch ya bayar da rahoton cewa wasu kasashe 10 daga cikin kasashen turai suna sauki ga musulmi fiye da sauran.

Kasashen kuwa sun hada da Poland da Italiya da kuma Hungary gami da girka da ma wasu kasashen na daban da ke kudanci da gabashin nahiyar turai.

Yayin da kasashen Birtaniya, Faransa da Jamus kuma muusulmi suka fi fuskantar nuna musu wariya da tsangwama da wasu daga cikin kasashen yammaci da arewacin nahiyar turai.

A kasar Amurka kuwa kididdiga ta yi nuni da cewa a cikin shekara ta 2014 kyamar da ake nuna wa musulmi ba ta kai wadda ake nuna musu ba ahalin yanzu, inda a cikin shekara ta 2017 kyamar musulmi ta rubanya a kasar Amurka.

Binciken ya tabbatar da cewa kyamar muuslmi ta karu ne a kasar Amurka bayan da ‘yan jamiyyar Republican mai mulki a yanzu suka karbi ragamar shugabancin kasar, wadanda kyamar musulmi na daya daga cikin siyasarsu.

3604767


captcha