Shafin labarai na Al-akhbar ya bayar da rahoton cewa, Majalisar malaman musulmi ta gudanar da taro kan ta'addanci da kyamar Musulunci a wurin baje kolin littafai na birnin Alkahira a jiya Alhamis 5 ga watan Fabrairu.
Babban daraktan majalisar Samir Boudinar ya kara da cewa: "Turai na tsoron musulmi 'yan ci-rani, kuma hakan ya faru ne saboda wasu matasa sun shiga kungiyar ta'addanci ta ISIL, kuma ISIL ta yi ikirarin cewa nahiyar Turai na da al'ummomi kafirai," in ji Samir Boudinar, babban daraktan majalisar, yana mai jaddada muhimmancin daukar hanyoyin kawo karshen kyamar Musulunci da ta'addanci, da hakan ya hada da saita tunanin wadannan musulmi masu gurbatacciyar fahimta.
Ya kara da cewa: Kungiyar ta'adda ta Daesh da tunani da akuma akidar wannan kungiya sun haifar da nuna wariya ga musulmi, da ma rarrabuwar kawuna ga musulmin bakin haure a kasashen turai, saboda wadannan musulmin ba 'yan asalin Turai ba ne.
Akidar Daesh dai ta samu asalinta ne daga akidar wahabiyanci mai tsanani da ke kafirta dukkanin musulmi matykar dai ba su shiga cikin kungiyar ba.
https://iqna.ir/fa/news/4033678