IQNA

Shugaba Assad Na Syria Ya Kada Kuri’arsa A Zaben Shugaban Kasa Da Ke Gudana A Yau A Kasar

23:10 - May 26, 2021
Lambar Labari: 3485951
Tehran (IQNA) shugaba Bashar Assad na Syria ya kada kuri’arsa a zaben shugaban kasa da ake gudanarwa a yau a fadin kasar ta Syria.

Shugaban kasar ta Syria wanda ya kada kuri’arsa a yau Laraba ya bayyana cewa; A lokacin da ‘yan ta’adda su ka mamaye yankin Doma, sun yi kokari gurbata sunan Syria, sai dai mazauna garin sun kasance masu tuntubar hukuma.

Shugaba Basshar Asad ya kara da cewa; Daga cikin mutanen birnin na Doma da akwai wadanda su ka yi shahada a cikin sojojin kasar.

Shugaban na kasar Syria wanda ya ziyarci birnin Doma domin kada kuri’ar zaben shugaban kasar da ake yi, ya kara da cewa; Ziyarar da ya kai Doma, tana kara tabbatar da cewa; Babu fada a tsakanin garuruwan garin, ko mabiya wata kungiya akan wata.

Da akwai ‘yan takara biyu da suke gogayya da Basshar Asad a zaben shugaban kasar da aka bude a yau Laraba.

 

 

3973946

 

 

captcha