IQNA

Kotun Afirka Ta Kudu Ta Bayar Da Damar Saka Lullubi Ga Jami’an Tsaro Musulmi Mata

23:57 - January 29, 2021
Lambar Labari: 3485601
Tehran (IQNA) kotun kasar Afirka ta kudu ta yanke hukunci da ya bayar da dama ga mata musulmi jami’an tsaro a kasar da su saka lullubi a kansu.

Tashar IOL ta bayar da rahoton cewa, a halin yanzu kotun kasar Afirka ta kudu ta yanke hukunci da ya bayar da dama ga mata musulmi jami’an tsaro a kasar da su saka lullubi a kansu da ma saka kaya da za su suturce jikinsu a yayin aiki.

Wannan na zuwa ne bayan karar da da wata musulma jami'ar 'yan sanda mai zuna Fatima Issacs ta shigar ne a gaban kotu, bayan da aka hana ta saka lullubi irin na musulunci a yayin aikinta.

An shigar da wannan kara ne tun a cikin shekara ta 2018, inda kotu ta ci gaba da bin kadun lamarin da kuma jin ta bakin lauyoyin wadda ta shigar da kara da kuma alkalai masana tsarin mulkin kasa.

Daga karshe dai a yau kotun ta yanke hukunci, wanda ya baiwa Fatima gaskiya, inda kotun tace ba laifi mba ne domin mata musulmi sun saka llubi a kansu a lokacin aiki, ko kuma saka sutura da za ta rufe jikinsu daidai koyarwar addininsu, amma dole kayan su zama daga irin kayan da ake yin amfani ne, nauinsu da kula.

Musulmi a kasar Afirka ta kudu sun yi farin ciki da wannan hukunci da kotun kasar ta yanke, wanda hakan zai iya ba mata musulmi damar shiga cikin ayyukan jami'an tsaro, wadanda a baya suke gudun shiga aiki saboda hana su saka tufafi daidai da koyarwar addinin musulunci.

3950435

 

captcha