IQNA

Ganawar Jagororin Kungiyoyin Gwagwarmaya Falastinawa

23:59 - February 19, 2020
Lambar Labari: 3484541
Tehran - (IQNA) jagororin kungiyoyin gwagwarmayar falastinawa na jihadul Islami da Hamas sun gana a Beirut Lebanon.

Kungiyoyin Jahadl-Islami da kuma Hamasa masu gwagwarmaya da Isra'ila sun sha alwashin kashe “Yarjejeniyar Karni” ta dukkan hanyoyin da suke da su.

Shafin yanar gizo na Filisdinul-Yaum ya nakalto babban sakataren kungiyar Jahadul-Islami da kuma tawagar kungiyar Hamas karkashin jagorancin Musa Abul-Marzuq suna fadar haka a yau Laraba bayan wani rahoton da suka fitar bayan ganawarsu.

Kungiyoyin sun kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka wanda ake kira “Yarjejeniyar Karn” ba zai taba samun nasara ba.  Shuwagabannin kungiyoyin sun kara da cewa zasu tabbatar da cewa wannan shirin bai kai ga nasara ba ta dukkan hanyoyin da suka samu.

Dangane da barazanar da gwamnatin Isra’ila takewa shuwagabannin kungiyoyin kuma, Hamas da Jahadul-Islami sun ce wannan ba zai tsoratasu ba.

Daga karshen kungiyoyin sun bukaci sauran kasashen larabawa da musulmi kada su maida hulda da Isra’ila a daidai lokacinda Falasdinawa suke jagorantar gwagwarmayan da yan mamaya.

3879986

 

captcha