IQNA

A Somalia An Kai Harin Bam A Kusa Da Fadar Shugaban Kasa

23:54 - December 22, 2018
Lambar Labari: 3483243
Bangaren kasa da kasa, Akalla mutane 7 aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kaddmar a yau a kusa da fadar shugaban kasar Somalia da ke birnin Mogadishu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, an kai harin ne da wata mota da aka shakare da bama-baai wadda ta tarwatse , kuma  nan take mutane bakwai suka rasu wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Tashar Universal ta sanar da cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da ma'aikatanta guda uku, daya daga cikinsu dan asalin kasar ta Somalia ne mai suna Awil Tahir, kuma yana da shedar zama dan kasa a Birtaniya.

Rahoton ya kara da cewa, an tayar da motar ne a wani wurin tsaro inda 'yan sanda ke gudanar da bincike, wanda yake yake tazarar kimanin mita 500 zuwa fadar shugaban kasar ta Somalia, kamar yadda kuma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da jami'an tsaron da suke aiki a wurin.

Kungiyar 'yan ta'addan wahabiyawa ta Alshabab mai alaka da kungiyar alkaida ta dauki alhakin kai harin.

3774491

 

 

 

captcha