IQNA

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar 10

23:56 - July 03, 2018
Lambar Labari: 3482805
Bangaren kasa da kasa, mayakn Boko Haram sun kasha sojojin jamhuriyar Nijar guda goma, tare da jikkata wasu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, hukumomin tsaro a Jamhuriya Nijar sun sanar da mutuwar sojojin kasar 10 da kuma batar wasu hudu da kuma uku da suka raunana, bayan wani hari da aka kai masu a yankin Diffa a kusa da tafkin Chadi.

Harin wanda ake danganta wa daga kungiyar Boko haram, an dai kai shi ne a cikin daren ranar Asabar data gabata a kauyen Bla Brin, dake nisan kilomita 40daga birnin N'Guigmi a kusa da yankin tafkin Chadi.

Mayakan sun kuma kone motocin soji masu yawa kafin su arce, kamar yadda kakakin ma'aikatar tsaron kasar, Kanal  Toure ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren.

3726968 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha