IQNA

Miliyoyin Musulmi Na Ziyara A Hubbaren Imam Ali (AS) A Najaf

23:49 - March 31, 2018
Lambar Labari: 3482527
Bangaren kasa da kasa, miliyoyin musulmi suna gudanar da ziyara a hubbaren Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf na kasar Iraki.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun a daren jiya ne miliyoyin musulmi mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka fara taruwa a hubbaren Imam Imam Ali (AS) da ke Najaf, domin halartar tarukan tunawa da zagayowar lokacin haihuwarsa.

A ranar 13 ga watan Rajab ne aka haifi Imam Ali (AS) wanda kuma wannan rana tana da matukar muhimamnci ga mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) inda suke raya ta da taruka na tunawa da wannan mutum mai girman matsayi a wurin Allah madaukakin sarki.

A daya bangaren kuma jami'an tsaron kasar Iraki sun dauki kwararan matakai na kare rayukan mutanen da suke gudanar da wadannan taruka na ziyara a hubaren Imam Ali (AS) a birnin na Najaf.

3702481

 

 

 

 

captcha