IQNA

An yi Maraba da aikin Alqur'ani na wani Ango a Masar

17:54 - November 18, 2022
Lambar Labari: 3488195
Tehran (IQNA) Masu ayyuka a shafukan sada zumunta sun wallafa wani faifan bidiyo na bikin auren wasu ma'aurata 'yan kasar Masar, wanda aka fara da karatun ayoyin Suratul Rum.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Sharrooq cewa, wannan aiki na ango a kasar Masar mai haske ya bai wa wadanda suka halarci bikin sha'awa.

Bayan fitar da faifan bidiyon, wasu sun taya wadannan matasa ma'aurata murna tare da bayyana cewa abin da ya fi kyau shi ne ango yana fara rayuwa da karatun ayoyin kur'ani mai girma.

 

 

 

 

 

 

4100353

Abubuwan Da Ya Shafa: ango shafin sadarwa yanar gizo halarci haske
captcha