IQNA

Matsayar Gwamnatin Falastinu Kan Kisan 'Yar Jarida Shireen Abu Akleh Da Isra'ila Ta Yi A Yau

17:00 - May 11, 2022
Lambar Labari: 3487278
Tehran (IQNA) Shugaban Falastinawa ya yi tir da Allawadai da kakkausar murya kan kisan da jami’an tsaron Isra’ila suka yi wa ‘yar rahoton tashar Aljazeera kuma fitacciyar ‘yar jarida ‘yar Falastinu, Shireen Abu Akleh.

ff

A cikin bayanin da ya fitar a yau, shigaban Falastinawa ya bayyana kisan nata a matsayin wani laifi daga cikin manyan laifukan da Isra’ila take aikatawa na kisan kiyashia akan al’ummar Falastinu.

Ya ce gwamnatin Isra’ila ce ke da alhaki kai tsaye a cikin wanann danyen aiki, wadda ta bayar da umarnin kashe falastinawa ko ta wane hali.

Jami’an sojin Isra’ila dai sun kashe Shireen Abu Akleh ne a lokacin da take aikin bayar da rahoto kai tsaye a yau Laraba daga garin Jinin da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda suka harbe ta a kai da harsashin bindiga, daga bisani kuma ta rasu.

Lamarin dai yana ci gaba da fuskantar tofin Allah tsinwe da Allawadai daga ko’ina cikin fadin duniya.

 

4056238

 

 

captcha