Daruruwan mutane ne fadin Amurka suka yi zanga-zangar nuna adawa da rawar da Facebook ke takawa wajen rura wutar kyamar musulmi da kuma cin zarafin mabiya addinin musulunci da 'yan addinin Hindu ke yi a India.
Daruruwan mabiya addinai daban-daban ne suka taru a manyan biranen Amurka guda takwas a ranakun Asabar da Lahadi don nuna adawa da shafin Facebook, inda suke zargin kamfanin da ba da damar yada kalaman kyamar musulmi musamman a Indiya, lamarin da ya kai ga cin zarafi, kai hare-hare da kuma kashe mabiya addinai marasa rinjaye da 'yan addinin Hindu ke yi.