Wakilin mabiya addinin kirista 'yan kabilar Arman a majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa, marigayi Imam Khomeini ya bayar da gudunmawa mai girma wajen gina al'umma ta hanyar yin amfani da hikima da ilimi da 'yan adamtaka da tsentseni da kuma adalci wajen yin jagoranci.