IQNA

Musulmin Faransa Suna Ci Gaba Da Fuskantar Takura A wuraren Aiki Da Wuraren Ibada

23:46 - June 13, 2021
Lambar Labari: 3486008
Tehran (IQNA) musulmin kasar Faransa suna ci gaba da fuskantar takura a wuraren ayyukansu da kuma wuraren ibada.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, wani bincike ya nuna cewa musulmin kasar Faransa suna ci gaba da fuskantar takura a wuraren ayyukansu da kuma wuraren ibada a kasar.

Rahoton ya ce cibiyar bincike ta Mountin a kasar Faransa ta gudanar da bincike, inda ta bayyana cewa, an samu karuwar nuna wa musulmi bambanci da kuma kyama a kasar Faransa a cikin shekara ta 2020.

Rahoton ya ce a kowane lokaci mata musulmi su ne suka fi fuskantar matsalar nuna musu bambanci da kyama, kasantuwar cewa su ne aka fi saurin gane cewa su musulmi ne, saboda saka tufafi na musamman da ke rufe jikinsu.

مسلمانان فرانسه در محیط کار و فرایض دینی که هر روز محدودتر می‌شود

Wani mai kamfanin sakar tufafi mai suna Bolval ya bayyana cewa, shekaru 20 da suka gabata suna tafiya kan tsarin da babu ruwansa da addini, amma yanzu suna la'akari da addini, musamman saka tufafi da mata suke yi, ba za su amince tufafin ya zama na wani addini a wurin aiki ba, saboda haka sun hana mata musulmi saka lullubi a kamfaninsu.

مسلمانان فرانسه در محیط کار و فرایض دینی که هر روز محدودتر می‌شود

Baya ga haka kuma a nata bangaren gwamnatin kasar Faransa, baya ga rufe masallatan musulmi da take yi da sunan cewa ana yin amfani da su wajen yada tsatsauran ra'ayi da ke kai wasu matasa musulmi zuwa ga shiga ayyukan ta'addanci, a daya bangaren kuma tana takura musulmi a sauran wuraren da ba a rufe ba, ta hanyar kafa musu dokoki da ka'idoji da kuma sanya ido a  kan dukkanin harkokinsu, da sunan matakan tsaro.

3977107

 

 

 

 

 

 

captcha