IQNA

An Rusa Sansanonin 'Yan Ta'addan Daesh 6 A Iraki

23:54 - June 06, 2021
Lambar Labari: 3485988
Tehran (IQNA) dakarun kasar Iraki sun rusa wasu manyan sansanonin 'yan ta'addan Daesh a cikin gundumar Samirra.

Tashar talabijin ta Akhbar Iraq ta bayar rahoton cewa, dakarun Hash Al-shaabi na kasar Iraki, tare da hadin gwiwa da jami'an tsaro na kasar, sun rusa wasu manyan sansanonin 'yan ta'addan Daesh a cikin gundumar Samirra.

Rahoton ya ce an kaddamar ad farmakin ne bayan samun bayanai da al'ummomin yankin, kan kai komo da mayakan 'yan ta'adda na Daesh suke yi a yankin, inda aka gano wanu manyan sansanoninsu guda 6 da suke kudancin lardin na Samirra, kuma aka ragargaza su.

Tun kafin wannan lokacin dai akwai bayanai kan yunkurin da kasashen ad suka wadannan 'yan ta'adda suke yi na neman sake farfado da su, domin ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a cikin Iraki da Syria, bayan karya lagonsu da aka yi a cikin wadannan kasashe.

Wasu daga cikin masu bin diddigin lamurran tsaro sun yi imanin cewa, sake farfado da 'yan ta'addan Daesh na daga cikin manufofin Amurka a Iraki.

 

3975760

 

captcha