IQNA

Jamus: An Dora Tubalin Ginin Wurin Da Zai Hada Wuraren Ibada Na Manyan Addinai

22:37 - June 03, 2021
Lambar Labari: 3485980
Tehran (IQNA) an dora tubalin ginin wurin da zai hada wuraren ibada na manyan addinai da aka saukar daga sama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan aiki an cimma matsayar gudanar da shi tsakanin malaman addinan kiristanci, da yahudanci da kuma musulmi a kasar Jamus, wanda a wurin za a gina masallaci, da majami’ar kiristoci gami da wurin bautar yahudawa.

An cimma wannan matsayar ne a wata tattaunawar addinai da ake gudanarwa a Jamus, wadda take hada jagororin mabiya wadannan addinai, inda bakinsu ya zo daya a kan samu wani babban wurin wanda za a gina dukkanin wuraren ibada na wadannana ddinai a cikinsa.

An kiyasta cewa aikin ginin wurin zai lakume kudi har euro miliyan 47, amma a halin yanzu akwai miliyan 20 da aka tanada domin fara aikin, wanda daga bisani za a kammala hada sauran kudaden.

Jagororin mabiya addinin musulunci da kiristanci da yahudawa  a kasar Jamus dai suna da kyakkyawar fahimta  a tsakaninsu, wanda hakan yana taimakawa matuka wajen samun zaman lafiya a tsakanin mabiya wadannan addinai a kasar.

3975332

 

captcha