IQNA

An Yanke Hukuncin Kisa A Najeriya Kan wani Mawaki Saboda Zargin Tozarta Matsayin Ma’aiki (SAW)

22:44 - August 11, 2020
Lambar Labari: 3485075
Tehran (IQNA) wata kotun addini ta yanke hukuncin kisa a kan wani mawaki bisa zarginsa da tozarta matsayin ma’aiki (SAW).

Kotun ta dauki wannan hukunci ne bayan da ta zargi mawakin dan shekaru 22 da haihuwa mai suna Yahya Aminu Sharif da yin wakar da ta tozarta matsayin manzon Allah (SAW).

A cikin wakar tasa wadda ya saka a shafukan zumunta, ya yabi wani daya daga cikin malaman darikar Tijjaniya, har ma ya kai shi ga wani matsayi wanda ya wuce na ma’aiki (SAW) wanda hakan ya harzuka jama’a da dama, sakamakon haka aka kame shi kuma aka yanke masa hukunci.

Kotun ta yanke masa hukuncin kisa ne ta hanyar rataya, duk kuwa da cewa dai zai iya daukaka kara a gaba zuwa wata kotun domin kalubalantar hukuncin.

Najeriya dai kasa ce da take da mabiya addinai daban-daban da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, kuma tsarin gwamnati a kasar ba shi da alaka da addini.

3915912

 

 

 

 

 

captcha