IQNA

Za A Bude Masallatai Dubu 4 Da Suka Cika Sharudda

21:04 - August 10, 2020
Lambar Labari: 3485072
Tehran (IQNA) Aljeriya ta sanar da cewa, gwamnatin ta bayar da marnin bude wasu daga cikin masallatan kasar bisa sharudda na kiyaye ka’idojin kiwon lafiya da aka gindaya.

Shafin yada labarai na Almasa ya bayar da rahoton cewa kwamitin malamai na kasar Aljeriya da gwamnati ta dorawa alhakin bincike kan yiwuwar sake bude masallatan kasar ya sanar da cewa, za a bude masallatai kimanin dubu hudu a kasar, wadanda suka cika sharuddan da ake bukata na kiwon lafiya.

Bayanin kwamitin ya ce; kimanin kashi 24 da zuwa kashi 25 na masallatan kasar ne a halin yanzu suka cika dukkanin sharuddan da aka gindaya, wanda yawansu ya kai kimanin dubu hudu, wadanda za a bude su a cikin wannan mako.

Haka nan kuma bayanin ya ce sallolin farilla ne kawai za a rika gudanarwa a cikin amasallatan na wani kayaadadden lokaci, kafin kiran salla da kuma bayan salla da mintuna goma za a rufe dukkanin masallatan a kowace rana.

Ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Aljeriya Yusuf Bilmahdi ya bayyana cewa, wannan mataki ya yi daidai, domin kuwa bai kamata a rufe masallatai da suka cika sharuddan kiyaye kamuwa daga cutar corona ba.

 

3915728

 

 

 

captcha