Shafin akhbar.net ya bayar da rahoton cewa, an saka kiran sallan ne daga dogon beni na Burj Khalifa da ke birnin Dubai a matsayin alamar bude masallatai a birnin.
Tun bayan bullar cutar corona dai aka rufe masallatai tare da hana gudanar da sallar jam’I, inda a halin yanzu aka bayar da damar bude masallatan amma bisa kiyaye sharuddan kiwon lafiya da aka gindaya.