IQNA

Mutanen Khartum Suna Karya Dokar Zama Gida A Cikin Ramadan

23:49 - April 26, 2020
Lambar Labari: 3484746
Tehran (IQNA) a daodai lokacin da aka fara udanar da azumin watana Ramadan al’ummar birnin Khartum na Sudan sun yi fatali da dokar zama gida.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, mutane da dama a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan sun fito dga gidajensu tare da karya okar hana zirga-zirga da kuma tilasta musu zama gida.

Inda jama’a da dama suka fito suka ci gaba da gudanar da hidimomi kamar yaddasuka saba a kowane lokacin azumin watan Ramadan, da hakan ya hada da yin sallolin jam’i bayan shan wa, da kuma yin buda baki tare.

Tun kafin wannan lokacin da gwamnatin kasar ta Sudan a kaa dokar hana fita daga gida  nuf dakile yaduwar cutar corona a kasar, wanda kafin watan Ramadan ya kama mutane suna yin aiki da dokar.

Ya zuwa jiya Asabar dai mutane 213 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar corona  akasar ta Suda, yayin da 17 daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya.

 

3894246

 

 

captcha