IQNA

Ayatollah Khatami: Tattakin Arbaeen Na Dauke Da Sakon Kur’ani

23:00 - October 11, 2019
Lambar Labari: 3484142
Bangaren siyasa, wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana Tattakin 40 na Imam Husain (AS) da cewa yana dauke da sakon kur'ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ayatullah Sayydi Ahmad Khatami ya kara da cewa; Wadanda suke yin tattakin na araba’in, mutane ne da zukatansu suke cike da kaunar iyalan gidan manzon Allah, wacce a wannan lokacin ta zama mara tamka a duniya.

Limamin na Tehran ya kuma ce; Adadin masu yin tattakin na bana ya kai miliyan 20, da za su yi tafiyar kasa ta tsawon kilo mita 80, wanda an saba yi a gama lafiya cikin nutsuwa.

Limamin na Tehran ya yi ishara da dukkanin makirce-makircen da makiya su ka shriya domin gani ba a yi tattakin na bana ba, sai dai hakan ba zai sa mutane su fasa ba, koda kuwa wane cikas za a gindaya a gabasu, saboda shaukinsu da Imam Husain (a.s).

A kowace shekara dai ana gudanar da taron arbaeen tare da halatar miliyoyin musulmi daga sassa daban-daban an duniya, domin nuna soyayya ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa, ta hanyar nuna alhini ga kisan da aka yi wa zuriyarsa.

 

3849019

 

 

 

captcha