IQNA

Firayi Ministan Sudan Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Yada Kiyayya a Kasar

23:54 - October 08, 2019
Lambar Labari: 3484131
Bangaren kasa da kasa, Abdullah Hamduk ya yi kira da a kawo karshen yada kiyayya da kuma tsatstsauran ra’ayi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya saka a cikin shafinsa na facebook, firayi ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya bayyana cewa, kasar Sudan kasa ce wadda ta hada mutane daban-daban, amma duk da haka tsarin kasa yana girmama mahangar kowa da addininsa da ra’ayinsa.

Wannan bayani na zuwa ne bayan wasu kalamai da daya daga cikin malaman salafiyya na kasar ta Sudan Abdulhay Yusuf ya yi ne, inda ya ce sabuwar gwamnatin hadin kasa da kasa da aka kafa ta zo ne domin rusa addinin musulunci a  Sudan.

Wanann furuci ya fusata da dama daga cikin al’ummomin kasar ta Sudan, wadanda suke ganin cewa dole ne gwamnatin kasar ta dauki kwararan matakan da suka dace domin dakile masu neman yin amfani da sunan addini domin haifar da wasu sabbin fitintinu a kasar.

Firayi ministan kasar ta Sudan ya jaddada cewa Sudan ba za ta taba komawa baya ba, kamar yadda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da dukkanin bangarori na al’ummar Sudan, ba tare da la’akari da banbancin addini ko mahanga ko akida ko kabila ba.

 

 

 

 

 

 

3847940

 

 

captcha