IQNA

An Gargadi Gwamnatin Jordan Kan Halartar Taron Bahrain

22:02 - June 17, 2019
Lambar Labari: 3483748
Masana da dama a kasar Jordan sun gargadi gwamnatin kasar kan halartar taron da Amurka da Isra’ila suka shirya gudanarwa a kasar Bahrain

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Yani Shafaq ya bayar da rahoton cewa, masana da dama da suka hada da malaman jami’oi har ma da wasu ‘yan siyasa  akasar Jordan, sun gargadi gwamnatin kasar da cewa, ta janye batun halartar taron Amurka da Isra’ila a Bahrain.

A cikin bayanai daban-daban dam asana na kasar Jordan da suka da lauyoyi da kuma kungyoyin farar hula suka fitar, sun bayyana halartar taron na bahraina  matsayin babbar yaudara ga al’ummar kasar, kuma cin amana ga al’ummar Palastine.

Kasashen larabawa da dama da aka aikewa goron gayyata domin halartar taron na Bahrain dai sun yi watsi da goron gayyatar, da suka hada da Iraki Lebanon da makamantansu, yayin da kasashen Saudiyya, hadadiyar daular larabawa, Bahrain, Jordan, masar da Morocco za su halarci taron.

3820103

 

 

 

 

 

captcha