IQNA

Mai Yiwuwa A Jinkirta Shirin Yarjejeniyar Karni

22:00 - June 17, 2019
Lambar Labari: 3483747
Fadar white house a Amurka ta sanar da cewa, mai yiwuwa a jinkirata shirin nan na yarjejeniyar karni zuwa wani lokaci a nan gaba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, babban jami’in gwamnatin Amurka kan harkokin gabas ta tsakiya Jason Greebaltt, ya bayyana cewa, mai yiwuwa za su daga batun shirin yarjejeniyar karni zuwa nan gaba.

Ya ce babban abin da ke gabansu a  halin yanzu shirya zaman taron birnin mana na Bahrain, domin tabbatar da cewa taron ya yi nasara kamar yadda aka shirya shi.

Dangane da batun yarjejeniyar karni kuwa wadda dama ita ce manufar taron, Greenblatt ya bayyana cewa, za a mayar da ita zuwa watan Oktoban wannan shekara.

Tun kafin wanna lokacin dai akwai masana Amurka da dama da suka hada har da ‘yan siyasa daga cikinsu, wadanda suke ganin cewa shirin yarjejeniyar karni ba zai yi nasara ba.

 

3819945

 

 

 

 

 

 

captcha