IQNA

A Najeriya Wani Hari Ya Lakume Rayukan Akalla Mutane 30

21:17 - June 17, 2019
Lambar Labari: 3483746
Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, akalla mutane 30 sakamakon tayar da wasu bama-bamai.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, majiyoyin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross sun sanar da cewa, an kai harin ne a daren jiya a wani gidan kallo, a lokacin da mutane suke kallon kwllon kafa a garin Konduga da ke kusa da birnin Maiduguri.

Rahoton ya ce kafin wannan harin an fara kai wani kusa da wani wurin sayar da shayi da ke garin, kuma dukkanin wadanda suka kai hare-haren mata ne.

Babu wata kungiya ko wani gungun jama’a da suka dauki alhakin kai harin, amma tuni an dora alhakin hakan a kan kungiyar Boko Haram wadda ita ce take kai irin wadannan hare-haren.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan furucin da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yi ne bayan rantsar da shi a wa’adin mulki na biyu, inda yake cewa sun samu nasara wajen karya lagon Boko Haram a kasar.

 

3820167

 

 

captcha