Kamfanin dillancin labaran iqna, a wata sanarwa ce da masu shigar da kara suka fitar a jiya Alhamis aka tabbatar da hakan, inda a ciki aka nemi a soma tuhumar shugaban, da sojoji suka kifar da mulkinsa bisa matsin lambar masu zanga zanga, kamar yadda kamfanin dilancin labaren kasar na Sunna ya rawaito.
Wata majiya wacce ta bukaci kamfanin dilancin labaren na Sunna, ya sakaya sunanta, ta ce ana tuhumar Al-Bashir da mallakar kudaden waje, da dukiya ta hanyar da bata dace ba, da kuma bada umarnin ayyana dokar ta baci a kasar.
A ranar ashirin da daya ga watan Afrilu da ta gabata, shugaban mulkin sojin kasar, Janar Abdel Fattah Burhane, ya sanar da cewa, an gano kudade da yawansu ya kai sama da dala miliyan dari da sha uku a gidan hambararen shugaban kasar.
3819574