IQNA

Sallar Idi Mafi Girma A Turai A Birnin Birmingham

23:51 - June 05, 2019
Lambar Labari: 3483712
An gudanar da sallar idi mafi girma a nahiyar turai baki daya wadda musulmi fiye da dubu 100 suka halarta a garin Birmingham da ke kasar Ingila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya abyar da rahoton cewa,ajiya ne gudanar da sallar idi mafi girma a nahiyar turai baki daya wadda musulmi fiye da dubu 100 suka halarta a garin Birmingham da ke kasar Birtaniya wanda kuam shi ne Karin farko da aka samu hakan.

An gudanar da wannan sallar idi ne dai a babban filin da ake kira Green lane Masjid, wanda wurin sakatawa da musulmi suke karbarsa a kowace salla domin yin sallar idi.

Daya daga cikin wadanad suke shirya gudanar da wannan sallar idi a wannan wuri ya bayyana cewa, wannan babbar dama ce ga dukkanin musulmin kasar Birtaniya, inda suke samu su hadu da juna su sada zumunci da kuma karfafa ‘yan wuwantaka.

A cikin shekara ta 2012 ne dai aka fara gudanar da sallar idi a birnin na Birmingham, tare da halartar musulmi dubu 12 a lokacin.

 

3817334

 

captcha