IQNA

Za A Ware Fan Biliyan Biliyan 24 Domin Sake Gina Makarantun Kur'ani A Sudan

22:51 - December 14, 2018
Lambar Labari: 3483216
Bangaren kasa da kasa, za a ware wasu makudan kdade domin sake gina wasu daga cikin makarantun kur'ani a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ma'aikatar kula da harkokin zakka  akasar Sudan ta sanar da cewa, ana shirin ware wasu makudan kdade domin sake gina wasu daga cikin makarantun kur'ani a kasar Sudan baki daya.

Bayanin ya ce wadannan kudade za a yi amfani da su domin yin gyara a makarantu 2381 da suka samu matsala, da kuma sake gina wasu da suka rushe, kamar yadda za a gudanar da wasu ayyukan da suka hada da ciyar da daliban kur'ani abinci.

Yanzu haka dai akwai daliban kur'ani kimanin dubu 300 a cikin wadannan makarantu da za a ware wadannan kudade domin su.

3772014

 

 

 

 

 

captcha