IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Habbaka Koyar Da Addini A Wasu Kasashen Afrika

23:56 - December 13, 2018
Lambar Labari: 3483213
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi tana goyon bayan habbaka harkokin koyar da addini a wasu kasashen Afrika.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, hafin yada labarai na Al’ain cewa, Yusuf Ahmad Bin Usaimin bababn sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa, kungiyar tana goyon bayan habbaka harkokin koyar da addini a wasu kasashen Afrika wato Gambia, Uganda da kuma Morosious.

Ya ci gaba da cewa, kungiyar tana da sabbin shirye-shirye na fadada ayyukanta a bangaren koyarwa a makarntu a kasashen Afrika, inda yanzu shirin zai fara daga wadannan kasashen.

Haka nan kuma kungiyar ta bude wani asusu na musamman domin gudanar da wadannan ayyuaka, inda kasashe masu karfi daga cikin kasashen musulmi.

3771943

 

 

 

 

captcha