IQNA

Gwamnatin China Na Takura Wa Muuslmi A Kasar

8:33 - December 11, 2018
Lambar Labari: 3483207
Bangaren kasa da kasa, Wani rahoton kungiyoyin kare hakkin bil adama ya nuna cewa, musulmi suna fuskantar takura daga mahukuntan kasar Sin a wasu yankunan kasar.

Gwamnatin China Na Takura Wa Muuslmi A KasarKamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na South China Morning ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da kungiyoyin suka mika wa kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, sun gabatar da bayanai kan yadda ake take hakkokin musulmi a kasar ta Sin.

Daga cikin bayanan da rahoton ya kunsa, akwai batun hana musulmi gudanar da harkokinsu na addini kamar yadda addininsu ya yi umarni, wanda hakan babban cin zarafi ne da kuma take hakkokin dana dam.

Kamar yadda kuma rahoton ya yi ishara da matakin da mahukunta a birnin Pingliang na kasar Sin suka dauka na rufe wata makarantar musulmi da ke birnin, inda suka bayar da wa'adi daga nan zuwa 17 ga wannan wata na Disamba da a rufe makarantar baki daya, ba tare da wani dalili mai gamsarwa ba.

An gina wannan makaranta ne tun a cikin shekara ta 1984, kuma musulmi suna gudanar da harkokinsu a wurin ba tare da an taba samun wata matsala da sub a, kamar yadda kuma makarantar da zama wurin koyon harshen larabci ga musulmi masu son koyon aikin tarjama ga 'yan kasuwa larabawa da ke zuwa kasar ta Sin domin harkokin kasuwanci, musamman daga yanking abas ta tsakiya.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da suka harhada wadannan rahotanni sun bukaci kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya da ya dauki matakin da ya dace kan wannan batu.

http://iqna.ir/fa/news/3770886

Abubuwan Da Ya Shafa: china muuslmi
captcha