IQNA

An Cafke Wani Mutum Da Ya Yi Harbi A Masallacin Annabi

23:53 - September 16, 2018
Lambar Labari: 3482988
Jami'an tsaron kasar Saudiyya sun sanar da cafke wani mutum wanda ya yi harbe-harbe da bindiga a cikin masallacin manzon Allah (SAW) a birnin Madina.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron na Saudiyya sun kame mutumin ne bayan da ya yi amfani da bindiga a cikin harabar masallacin annabi (SAW) a daren jiya Asabar, inda ya firgita jama'a da suke a wurin.

Rahoton ya ce babu wanda ya rasa ransa ko samun raunuka sakamakon hakan, kuma yanzu haka yana tsare a ofishin bincike na rundunar 'yan sanda da ke birnin Madina.

Wasu daga cikin wadanda suka sheda abin da ya faru sun bayyana cewa, mutumin wanda babu wanda ya san shi a wurin, ga dukkanin alamu yana fama da matsalar tabuwar hankali.

3747226

 

captcha