IQNA

Falastinawa Za Su Dauki Matakan Kalubalantar Dokar Mayar Da Palastinu Kasar Yahudawa

23:36 - September 12, 2018
Lambar Labari: 3482977
Wakilan larabawa a majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset sun sanar da cewa, al'ummar Palastine ba za su taba amincewa da dokar mayar da Palastine kasar Yahudawa ba.

 

Shafin yada labarai na Albawwaba News ya habarta cewa, Jamal Zahalika da kuma Ahmad Tayyibi sun sanar da cewa, wadanda 'yan majalisar dokokin Isra'ila ne da ke wakiltar larabawa, sun jaddada cewa dukkanin al'ummar Palastinu na daram a kan baknasu an kin amincewa da dokar da ke nufin mayar da Palastine kasar yahudawa zalla.

Jamal Zalika ya ce a ranar daya ga watan Oktoba mai kamawa Falastinawa za su shiga yajin aiki a dukkanin yankunansu, domin nuna rashin amincewa da dokar mayar da Palastinu kasar yahudawa, da kuma nuna rashina mincewa da shirin nan na yarjejeniayr karni, wanda ke nufin amincewa da quds a matsayin babban birnin Isra'ila, da kuma saryar da hakkin miliyoyin Falastinawa da aka kora dawowa gida.

Haka nan kuma Zahalika ya kara da cewa, za su mayar da kowace ranar 19 ga watan a Yuli a matsayin ranar yaki da wariya, kasantuwar a wannan ranar ce a cikin watan Yulin wannan shekara ta 2018, majalisar Knesset ta amince da dokar amincewa da Palastinu da yahudawa suka mamaye a matsayin kasar yahudawa.

3746193

 

 

 

captcha