Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a zaman da majalisar Knesset ta haramtacciyar kasar Israila ta gudanar a jiya, an kada kuri’a kan daftarin dokar haramta yada duk wani kisa ko cin zarafi na jami’an tsaron Isra’ila akan Falatinawa.
Mambobi 45 daga cikin mamobin majalisar sun amince da daftarin kudirin, yayin mambobi 42 suka ki amincewa da shi.
Dokar dai ta kunshi cewa, idan aka kama wani yana yada hotuna ko kuma hotunan bidiyo na wani aikin cin zarafi da jami’an tsarin Isra’ila suke yi kan Falastinawa, to za a daure shi daga shekaru 5 zuwa 10 a gidan kaso.
Yusuf Jabbarin daya ne daga cikin ‘yan majalisar Knesset ta Isra’ila daga cikin wakilan larabawa, wanda ya bayyana hakan da cewa yunkuri ne na boye muggan laifukan da sra’ila take akatawa kan al’ummar Palastine, kuma ba za su taba amincewa da hakan ba.