IQNA

Qasemi: Amurka Ba Ta Da Matsayin Za Ta Bata Fuskar Wasu Kasashe A Idon Duniya

23:45 - June 19, 2018
Lambar Labari: 3482771
Bangaren kasa da kasa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya mayar da martani dangane da sukar da Amurka ta yi kan zartar da hukuncin kisa a kan wani da ya jagoranci kisan jama'a a Tehran.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Qasemi ya bayyana cewa; zartar da hukuncin kisa da aka yi yau a Iran a kan Reza Salas, an yi sa ne bisa ka'ida, domin kuwa ya amsa dukkanin laifukan da ake zarginsa da aikatawa, kuma lauyoyinsa sun yarda da hakan, amma sun bukaci a sassauta hukuncin ne kawai, wanda kuma alkali ne yake da hakkin zartar da hukunci na karshe.

Reza Salas ya amsa cewa shi ne ya jagoranci wasu matasa da suka tayar da tarzoma a wasu lokutan baya a wata unguwa a cikin Tehran, inda suka kashe jami'an tsaro uku har lahira, tare da jikkata jama'a da dama mazauna unguwar, kamar yadda kuma suka lalata kaddarorin gwamnati da na jama'a da dama.

Mutumin ya amsa cewa yana daga cikin wadanda suka aiwatar da kisan jami'an tsaron, kuma an yanke masa hukunci ne bisa amsa laifin kisan kai da ya yi.

Qasemi ya ce Amurka ba ta da hurumin da zata zargi Iran da take hakkin 'yan adam a kan wanann batu, domin ita ce mi mai take hakkokin 'yan adam da yi musu kisan kiyashi a kasashen duniya kamar yadda kowa ya sa hakan.

Haka Kuma Qasemi ya bayyana tsanin kiyayyar da Trump yake nuna wa bakin haure da kwace 'ya'yansu da ake yi da cewa shi ne babban cin zarafin 'yan adam, wanda hatta matarsa da ma sauran masu mara masa baya  acikin fadar white house duk sun yi Allawadai da shi kan hakan.

3723883

 

 

 

captcha